[News] A Letter To Governor Ganduje by Mr Auta


BUDADDIYYAR WASIKA ZUWA GA GWAMNAN KANO
#
#
daga Mr. Auta
Aka MURYAR NAKASASSU

Mai girma gwamnan kano Dr Abdullahi umar ganduje kadimul Islam, kasancewarka uba kuma jagora sannan mai fada aji ya kamata inma magana ta sigar da zaka fahimta, kokarin kare mutuncinka Kai da kanka ba shine martabar cikar kamalarka ba, kamata yayi ka kokarta kare hakkin al'ummarka su kuma sai su kare mutuncin ka, batu nake akan kashin bayan kowacce Al'umma wato kananan yara, daya kawai! Akan daya kawai kuma itama da amincewarta hankalin kowanni mai mulki ya Gaza kwanciya a arewa, munaji muna gani aka bada shi ya fuskanci hukunci, amma yau Tara! Wayanda inda za'a tsaurara bincike ma sunfi haka abisa tilastawa batare da amincewa bah ake sacesu akaisu kudu ba kuma anan aka tsaya bah asa suyi ridda sannan adinga azabtar dasu INNALILLAHI amma yau ankama masu aikata haka sannan manyan arewa su kara gyara kwanciya tare da kafafen yada labarai, toh INA amfanin gwagwarmayar da mukasha wajen zabanka a shugaba? Mai girma gwamna wannan bafa batun da ya shafi gwamnatin tarayya bane batu ne da ya shafi gwamnatin jaha, kana da iko da kuma martabar da fadarka ta second talatin kawai ya isa yasa kowanni gidan jarida ya farka sannan muma muji dadin kace wani Abu

A karshe inaso ka sani IDAN TURI YAKAI MAKURA JUYOWA AKE munada karfin da zamu iya tsayar da komai na kano har sai an farka akan lamarin nan ta hanyar tada zanga-zangar lumana, amma mukaki haka dan kasancewarmu masu koyi da fadar magabatanmu,
Muna fatan zaka magantu akan wannan matsalar tamu
Mun barka lafiya mai girma gwamna

Pls mai karantawa in sakona ya sameka ka tayani share har sakon yaje inda akeso ya karasa

Daga Mr. Auta
Aka MURYAR NAKASASSU

Click Here To View

Comments

Popular posts from this blog